Burundi

Ana zargin tsaffin hafsoshin Burundi da kisan shugaba Melchor Ndadaye

Tsohon shugaban kasar Burundi, kuma zababben shugaban kasar na farko Melchior Ndadaye, wanda 'yan kabilar Tutsi suka hallaka a juyin mulkin da bai yi nasara ba a ranar 21 ga Oktoba na shekarar 1993.
Tsohon shugaban kasar Burundi, kuma zababben shugaban kasar na farko Melchior Ndadaye, wanda 'yan kabilar Tutsi suka hallaka a juyin mulkin da bai yi nasara ba a ranar 21 ga Oktoba na shekarar 1993. ANP/AFP Dabrowski

Gwamnatin Burundi tace ta kama wasu tsaffin hafsoshin sojin kasar 4 bisa zarginsu da hannu wajen kashe zababben shugaban kasar na farko Melchor Ndadaye.

Talla

Wadanda aka kama sun hada da Janar Celestin Ndayisaba, Kanal Gabriel Gunungu, Kanal Laurent Niyonkuru da kuma Kanal Anicet Nahigombeye.

Mai gabatar da kara Sylvester Nyandwi yace an bude bincike ne sakamakon bayanan da suka samu na karin masu hannu a kisan gillar da aka yiwa tsohon shugaban ranar 21 ga watan Oktoba a shekarar 1993.

Wani bincike da kungiyar kasashen Afirka ta AU ta gudanar, ya bankado cewar hafsoshin sojin kasar ne suka hallaka shugaban wanda ya fito daga kabilar Hutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.