Harin kunar bakin wake ya jikkata mutane 29 a Kamaru

Sojojin yaki da ta'addanci da ake kira BIR a kasar Kamaru a yankin waza na kasar a  2014.
Sojojin yaki da ta'addanci da ake kira BIR a kasar Kamaru a yankin waza na kasar a 2014. AFP PHOTO / REINNIER KAZE

Majiyoyin tsaron Kamaru sunce mutane akalla 29 suka jikkata, bayan da wata ‘yar kunar bakin wake ta tarwatsa kanta, a lardin Arewa mai Nisan kasar.

Talla

Shedun gani da ido suka ce, 'yan kunar bakin waken biyu ne suka iso garin Amchide mai makwabtaka da Najeriya, inda sojoji sukayi nasaran harbe daya daga cikinsu kafin daya kuma ta tada jigidan da ke jikinta.

Wani dan kato da gora ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewar, an kai harin ne da sanyin safiya a kasuwar garin na Amchide, a ranar da kasuwar mako ke ci.

Garin Amchide na daya daga cikin manyan garuru da ke samar wa kasar kudin shiga kafin al’amura su tabarbare a shekarar 2014, sakamakon mamaya da mayakan Boko-Haram sukayi wa yankin, abin da ya tilastawa mazauna yankin kauracewa gidajensu, inda suka nemi mafaka a wasu sassar kasar.

Kuma wannan harin yakara sanya fargaba a zukatan al’umma, a yayin da ‘yan gudun hijiran yankin suka fara dawowa gida, ganin zaman lafiya da aka samu, sakamakon kafa sansanonin soji da hukumomin Kamaru sukayi, ga kuma sojojin kawancen kasashen Kamaru da Najeriya da Tchadi da ke aiki a yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.