Faransa-Rwanda

Kotu ta kara soke binciken rawar da sojan Faransa suka taka a kisan kiyashin Rwanda

Dakin hotunan  tarihin tunawa da kisan kiyashin Rwanda dake Kigali.
Dakin hotunan tarihin tunawa da kisan kiyashin Rwanda dake Kigali. AFP PHOTO / SIMON MAINA

ALKALAN Faransa sun ki amincewa da wata bukata da mutanen da suka tsira daga kisan kiyashin da akayi a Rwanda, a shekarar 1994, suka gabatar na sake gudanar da bincike cewa sojojin Farnsa na da hannu wajen kashe daruruwan fararen hular da suka yi alkawarin kare rayuwar su.

Talla

A cikin wani kudiri da aka fitar a ranar 22 ga wannan wata na, alkalan kotun shara’ar manyan laifukan yaki da na keta rigar mutuncin dan adam, su uku sun yi watsi da daukacin bukatar da kunkiyoyin kare hakkin dan adam suka shigar, inda suke bukatar sake farfado da binciken da aka kaddamar kuma aka rufe a kakar bana

A shekara 2005, Kungiyoyin kare hakin dan adam na duniya, da suka hada da Survie, (FIDH da kuma LDH), suka zargi sojan Faransa da barin daruruwan yan kabilar Tutsi ga hannun dakarun kisan kiyashi na gwamnatin yan Hutu, da ke samu goyon bayan Faransa suka yi masu kisan gilla a tsaunukan Bisesero dake yammacin a ranakun 27 zuwa 30 ga watan yunin 1994,

A 2005 ne mutanen da suka tsira da rayukansu daga kisan kiyashin ne suka shigar da karar dakarun na Faransa a gaban kotu, sakamakon kasa basu kariyar da ta dace duk kuwa da alkawulan da suka dauka na kare rayukan fararen hular yan kabilar Tutsi, inda a cikin kwanaki uku makasa yan hutu suka yi masu kisan gilla mafi muni da aka taba gani a nahiyar Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.