Kamaru-Wasanni

Kamaru ta rasa damar karbar bakoncin gasar cin kofin Afrika

Hukumar CAF dai kai tsaye ba ta sanar da kasar da za a mika gasar ba, sai dai ta ce za ta sanar da hakan kafin karshen shekarar nan.
Hukumar CAF dai kai tsaye ba ta sanar da kasar da za a mika gasar ba, sai dai ta ce za ta sanar da hakan kafin karshen shekarar nan. PACOME PABANDJI / AFP

Hukumar kwallon kafar Afrika CAF ta sanar da matakin karbe ragamar daukar nauyin bakoncin gasar cin kofin nahiyar da zai gudana badi daga hannun Kamaru.

Talla

CAF wadda ke sanar da wannan mataki bayan wani taron sirri da shugabanninta suka shafe tsawon sa’o’I 10 suna gudanarwa yau a birnin Accra na kasar Ghana, ta ce duk kasar da ke da sha’awar karbar bakoncin gasar ta na iya mika bukatar hakan don fara tantancewa da nufin gano kasar da za ta iya jan ragamar gasar a badi.

Shugaban hukumar Ahmad Ahmad a taron manema labaran da ya kira yau din nan, bai ambaci sunan kasar da za a mika gasar ba kai tsaye amma ya ce kasashen Morocco da Afrika ta kudu na daga cikin wadanda suka fara nuna sha’awar karbar bakoncinta.

Morocco dai ta rasa damar karbar bakoncin gasar cin kofin duniya ta 2026 wanda kuma sai da ta kammala shiryawa gasar amma ta rasa damar, wanda ake ganin matakin na CAF ka iya zame mata damar da ta k enema.

A bangare guda itama Afrika ta kudu ana ganin za ta iya karbar gasar la’akari da yadda ta karbi bakoncin wasannin cin kofin duniya na 2010 dama na gasar Nations League a 2013.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI