Burundi-Tanzania

Shugaban Burundi ya kauracewa taron kasashen yankin

Pierre Nkurunziza  shugaban kasar Burundi
Pierre Nkurunziza shugaban kasar Burundi REUTERS/Evrard Ngendakumana

Shugaban Burundi Pierre Nkurunziza, ya ce ba zai halarci taron da shugabannin kasashen yankin gabashin Afirka da za su gudanar yau juma’a a birnin Arusha na Tanzania .

Talla

Nkurunziza ya ce ba a sanar da shi cewa za a gudanar da wannan taro a kan lokaci ba, yayin da bayanai ke cewa ga alama shugaban ba ya son haduwa zaure daya da takwaransa na Uganda saboda tsamin danganta, yayin da shekaru biyu da suka gabata aka yi yunkurin kifar da gwamnatinsa a lokacin da yake halartar irin wannann taro na shugabannin kasashen yankin gabashin Afirka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.