Afrika

Taron kawo karshen kungiyar Boko Haram

Taron Shugabannin kasashen Tafkin Chadi
Taron Shugabannin kasashen Tafkin Chadi Bashir Ibrahim Idris

Shugabannin Kasashen Tafkin Chadi sun bukaci taimakon kasashen Duniya wajen murkushe mayakan kungiyar Boko haram da yanzu haka ke zafafa hare haren dake kashe jama’a a yankin ba tare da kaukautawa ba.

Talla

Bayan wani taron da suka yi a N’djamena da ya samu halartar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da takwarorin sa na Nijar, Mahamadou Issufou da Idris Deby na Chadi da kuma Firaministan Kamaru Philemon Yang, shugabannin sun ce suna bukatar karin taimakon kasashen Duniya domin shawo kan matsalar.

Shugabannin sun bukaci sake fasalin yakin a tsakanin dakarun su da kuma hadin kai wajen musayar bayanan asiri.

Taron ya samu halartar manyan hafsoshin sojin rundunar hadin kai ta musamman dake yaki da Boko haram wadda ke da cibiya a N’djamena.

Alkaluman Majalisar Dinkin Duniya sun nuna cewar mutane sama da 27,000 suka mutu sakamakon yakin, yayin da kusan miliyan biyu suka rasa matsugunin su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.