Cutar Ebola ta tafka barna a Jamhuriyar Congo - WHO
Wallafawa ranar:
Hukumar lafiya ta duniya WHO ta bayyana annobar cutar Ebola da ta sake barkewa a Jamhuriyar Congo a matsayin wadda ke mataki na biyu mafi muni a tarihi, bayan annobar cutar da ta hallaka dubban jama’a a Afrika ta Yamma cikin shekarun baya.
Rahoton na zuwa ne a dai dai lokacin da ma’aikatar lafiyar jamhuriyar Congo ta sanar da cewa, yawan wadanda suka kamu da cutar ta Ebola a baya bayan nan ya kai 426.
Kawo yanzu dai ma’aikatar lafiyar ta Congo, tace mutane 198 cutar ebolan ta hallaka, tun bayan sake bullarta a ranar 1 ga watan Agustan da ya gabata.
Cutar dai tafi shafar garin Beni dake gabashin kasar, da kuma lardin Kivu a arewaci, wadanda ke fama da hare-haren kungiyoyin mayaka, lamarin da ya dakle kokarin jami’an lafiya wajen magance yaduwar cutar a yankunan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu