Najeriya-Rashawa

Kotun Najeriya ta nemi EFCC ta gurfanar da Diezani gabanta

Tsohuwar ministar man fetur a Najeriya Diezani Allison-Madueke wadda yanzu haka ke fuskantar tuhumar rashawa.
Tsohuwar ministar man fetur a Najeriya Diezani Allison-Madueke wadda yanzu haka ke fuskantar tuhumar rashawa. AFP / Wole Emmanuel

Wata Kotu a Abujar Najeriya yau ta bai wa hukumar EFCC damar gurfanar da tsohuwar ministar mai Diezani Alison Madukwe da tsohon shugaban kamfanin hakar mai Olajide Omokore a gaban ta saboda zargin hada baki da kuma halarta kudaden haramun.

Talla

Mai shari’a Valentine Ashi ta bukaci gabatar da mutanen biyu ranar 25 ga watan Fabarairu shekara mai zuwa, bayan da mai gabatar da kara Faruk Abdullahi ya shaida mata cewar ana cigaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Daga cikin tuhumar da ake yi wa minista harda karbar gidaje na kasaita a matsayin cin hanci da rashawa.

Sai dai lauyan tsohuwar ministar, Tayo Adeniyo ya ce ba’a mika musu takardar tuhumar da ake wa tsohuwar ministar ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI