Janar Idris Bello Dambazau kan yawan sojojin Amurka a nahiyar Afrika

Sauti 03:28
Daya daga cikin dakarun Amurka na musamman dake horar da dakarun sojin Jamhuriyar Nijar a yankin Diffa. 4/Maris/2014.
Daya daga cikin dakarun Amurka na musamman dake horar da dakarun sojin Jamhuriyar Nijar a yankin Diffa. 4/Maris/2014. REUTERS/Joe Penney/File photo

Wani bincike ya bayyana cewar duk da ikrarin Amurka cewar sojin ta basu da yawa a nahiyar Afirka, bayanai sun tababtar da cewar rundunar sojin Amurka dake da cibiya Afirka da ake kira Africom na da cibiyoyi 34 a kasashe daban daban.Takardun bayanan da The Intercept ta samu sun ce Amurka da sansanonin soji a kasashen Nijar da Libya da Somalia da Kamaru da Mali da Chadi da Uganda da makaman tan su.A Jamhuriyar Nijar rahotan yace Amurka na da sansanoni 5 cikin su harda Agadez da Ouallam da Arlit da Maradi.Akan wannan Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Janar Idris Bello Dambazau, kuma ga yadda hirar su ta gudana.