Isa ga babban shafi
Najeriya

Adadin sojin Najeriya da suka mutu a Buni Gari

Muhammadu Buhari Shugaban Najeriya tareda wasu manyan hafsan sojin kasar a Maiduguri
Muhammadu Buhari Shugaban Najeriya tareda wasu manyan hafsan sojin kasar a Maiduguri Dailymonitornig/rfi
Zubin rubutu: Abdoulaye Issa
Minti 1

Rundunar Sojin Najeriya ta tabbatar da mutuwar sojin ta guda 8 lokacin da mayakan boko Haram suka kai musu hari a sansanin su dake Buni Gari a Jihar Yobe.

Talla

Kamfani dillancin labaran Faransa ya ce daraktan yada labaran rundunar Janar Sani Usman Kukasheka ya tabbatar masa da aukuwar lamarin.

A karshen makon da ya gabata ne mayakan book Haram suka kai harin, wanda ke zuwa kwanaki bayan na Matelel.

A lokacin da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ziyarci Maiduguri ya sha alwashin yin amfani da duk wata dama da tsarin mulkin Najeriya ya tanadar masa wajen samar da kayan yaki na zamani don kawo karshe abinda ya bayyana da haukar da mayakan Boko haram ke yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.