Afirka

Amurka zata rage yawan sojin ta a Afirka

Tutar Amurka
Tutar Amurka

Shugaban rundunar sojin Amurka dake aiki a Afirka, Janar Roger Cloutier yace shirin rage yawan dakarun dake aiki a Nahiyar ba zai shafi ayyukan da suke gudanarwar ba.Ma’aikatar tsaron Amurka ta bayyana cewar zata rage kashe 10 na sojojin Amurka 7,200 dake gudanar da aikace aikace daban daban a Afirka.

Talla

Janar Cloutier wanda ya tabbatar da cewar sojin Amurka yanzu haka na cikin kasashe akalla 40 dake Afirka, yace suna bada horo da kuma taimakawa kawayen su amma ba yaki ba.

Cloutier wanda ya jagoranci bincike kan yadda aka kashe sojojin kasar a Nijar yace sun koyi darasi kan abinda ya faru.

Rundunar Sojin Amurka ta ladabtar da wasu jami’an ta guda 6 saboda rawar da suka taka wajen kuskuren da ya faru a Jamhuriyar Nijar bara wanda ya yi sanadiyar kashe sojojin kasar guda 4 tare da na Nijar guda 5.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI