EU-Afrika

EU ta zargi kasashen Afrika da karkatar da kudaden tallafi

Shugaban SenegalMacky Sall tare da shugaban majalisar zartarwa na EU Donald Tusk da kuma Fira Ministan kasar Malta Joseph Muscat yayin taron shawo kan matsalar Bakin-Haure a birnin Valletta dake kasar Malta. 12/11/2015.
Shugaban SenegalMacky Sall tare da shugaban majalisar zartarwa na EU Donald Tusk da kuma Fira Ministan kasar Malta Joseph Muscat yayin taron shawo kan matsalar Bakin-Haure a birnin Valletta dake kasar Malta. 12/11/2015. REUTERS/Darrin Zammit

Tawagar masu binciken kudade ta kungiyar Tarayyar Turai EU, ta ce gwamnatocin kasashen Afrika, na karkatar da tallafin da take basu kan inganta fannonin samar da abinci, tsaro, Ilimi da lafiya, zuwa wasu bukatu na son rai.

Talla

Binciken na baya bayan nan ya fi mayarda hankali ne akan kasashen Libya da Nijar, inda wakilan na EU suka bi diddigin yadda hukumomin kasashen suka yi amfani da kudaden tallafin da aka mika musu, a nan kuma suka gano rashin mayar da hankali wajen yin amfani da tallafin yadda ya kamata ko ma kautar da shi daga makasudin a wasu lokutan.

A shekarar 2015 kungiyar kasashen tarayyar Turai ta kafa gidauya mai sunan EUTF domin magance tushen matsalolin da suka haddasa kwarar dubban bakin haure zuwa nahiyar, da kuma yawaitar ‘yan gudun hijirar cikin gida a sassan Afrika.

Daga waccan lokacin da aka kafa ta zuwa yanzu, gidauniyar ta EUTF ta tara kudi kimanin Euro biliyan 4 da miliyan 100, wanda daga cikinsa take baiwa kasashen nahiyar Afrika 26 tallafin bunkasa sha’anin tsaro, lafiya, ilimi da kuma ayyukan gona.

Kasashe 26 dake samun tallafin kuwa sun fito ne daga yankunan Afrika da suka hada da Sahel, yankin Tafkin Chadi, arewaci da kuma gabashin nahiyar, sai dai kasashen Libya da Jamhuriyar Nijar ke kan gaba wajen samun kaso mafi tsoka na daga cikin tallafin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI