Guinea Bissau

An dakatar da rijistan masu zabe a Guinea Bissau

José Mário Vaz, Shugaban kasar Bissau Guinea
José Mário Vaz, Shugaban kasar Bissau Guinea ONU/Cia Pak

Kotun kasar Guinee Bisseau ta sanar da dakatar da rijistan masu zabe,bisa zargin cewa da sauran gyara da ya dace a kawo zuwa ga na’urorin zabe da aka shigo da su kasar.

Talla

Matakin da alkali mai shigar da kara na gwamnati ya dau na biyo bayan wani bincike da ya gudana yan lokuta bayan da wasu jam’iyyun siyasa suka bukaci ganin an dakatar da yiwa masu zabe rijista.

Dakatar da ci gaba da rijistan masu zabe a kasar ta Guinee Bissau zai haifar da jikiri a zaben kasar a cewar manzo na musaman daga Majalisar Dinkin Duniya na yankin afrika ta yamma Mohamed Ibn Chambas.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.