Uganda-Ebola

Uganda ta yi riga-kafin Ebola ga jami'an lafiyarta dubu 3

Wannan dai ne karo na 10 da Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo ke fuskantar annobar cutar ta Ebola.
Wannan dai ne karo na 10 da Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo ke fuskantar annobar cutar ta Ebola. REUTERS/Tommy Trenchard

Ma’aikatar lafiya a Uganda ta ce kawo yanzu ta yi riga-kafin cutar Ebola ga jami’an lafiyarta akalla dubu 3, galibi wadanda ke aiki gab da kan iyakar kasar da Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo da ke fuskantar annobar cutar.

Talla

Tun a watan da ya gabata ne Ugandar ta dauki matakin rigakafi ga jami’an lafiyar kafin daga bisani ta koma kan fararen hula wanda ta ce shi ne kadai hanyar kare al’ummar kasar daga fuskantar cutar yayinda su ke da tazarar kilomita 50 kacal da yankin da cutar ta fi tsananta a Congo.

Yanzu haka dai cutar Ebolar ta hallaka mutane 268 a barkewarta ta baya-bayan nan a gabashin yankin Beni da ke gab da kan iyakar Ugandar da Jamhuriyyar demokradiyyar Congo.

Wannan dai ne karo na 10 da cutar ke barkewa a Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo tun bayan gano ta a duniya baki daya, yayinda cutar ke barazanar fantsamuwa zuwa makotan kasashe la'akari da yadda ta ke saurin kisa a wannan karon.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI