Nijar-Najeriya

Nijar na fatan samar da horo zuwa Dakarun kasar

Shugabannin kasashen Nijar,Chadi da Najeriya a taron kasashen Afrika a Mauritania
Shugabannin kasashen Nijar,Chadi da Najeriya a taron kasashen Afrika a Mauritania rfi hausa

Ministan tsaron Jamhuriyar Nijar Kalla Moutari ya bayyana cewa ya dace a samar da horo zuwa jami’an tsaro domin kasancewa cikin shirin ko ta kwana ,da alama a shekara mai kamawa ,shekarar 2019 kungiyar Boko Haram za ta yawaita kai hare-hare gani yawan makaman da kungiyar keda su yanzu haka.

Talla

Ministan ya bayyanawa yan Majalisu kasar cewa kungiyar Boko Haram na da yawan makamai da kuma zata iya amfani da su a hare-haren da zata kai zuwa Nijar dama wasu kasashe.

Ministan tsaron Nijar Kalla Mountari na Magana ne a zauren Majalisa a lokaci da yake gabatar da yanayin tsaro na yankin Diffa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI