Morocco

Yan Sanda sun kama hodar iblis kg 1000

Hodar Ibilis
Hodar Ibilis Getty images/Jose Azel

Yan Sandan Morocco a jiyar asabar sun sanar da kama kusan kilogramme 1000 na hodar Iblis tareda capke mutane 7 a wani samame da suka kai a gabar ruwan kasar a dai dai lokacin da aka jibge hodar cikin wani jirgin macinta a El Jadida.

Talla

Karo na farko da yan Sanda a kasar Morocco suka yi irin wannan kame,rahotanni sun bayyana cewa an shigo da wannan hodar ne daga yankin Latino Amurka.

Hukumomin kasar sun umurci yan Sanda da su gudanar da bicinke domin gano masu hannu a wannan kazamin aiki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.