Najeriya-Zabe

Yakubu Dogara ya zargi Buhari da saye kuri'un talakawa

Shugaban Majalisar wakilan Najeriya Yakubu Dogara.
Shugaban Majalisar wakilan Najeriya Yakubu Dogara. NAN

Shugaban Majalisar wakilan Najeriya Yakubu Dogara ya zargi gwamnatin Muhammadu Buhari da yunkurin saye kuri’un talakawan kasar karkashin shirinta na TraderMoni da ke ikirarin bayar da jari ga marasa karfi, dai dai lokacin da babban zaben 2019 ke karatowa.

Talla

A wani taron jin bahasin jama'a da kwamitin yaki da sayen kuri'u na hukumar zaben Najeriyar ya gudanar yau Litinin, Dogara ya ce kai tsaye za su bayyana shirin na Muhammadu Buhari a wani matakin Cin hanci da rashawa.

A cewar Yakubu Dogara shirin na Muhammadu Buhari da bai kankama ba sai yanzu da zaben kasar ya karato ya sabawa sashe na 124 (1) a da b da c da kuma sashe na (124) da (2) da (4) da (5) dama sashe na 130 na zaben Najeriyar.

Shirin wanda mataimakin shugaban Najeriyar Yemi Osinbajo ya kaddamar a da dama daga cikin sassan kasar na karkashin wani tsarin gwamnati don samar da ayyukan yi da kuma agazawa ‘yan kasuwa marasa jari wanda aka ware masa wani adadi na kudi a kasafin kudin shugaban na farko bayan hawa madafun iko.

Kafin yanzu dai makamancin wannan koke daga shugaban Majalisar Dattijan Najeriyar Bukola Saraki, wanda ke ganin Buharin na amfani da damar don janyo hankalin al'ummar kasar su kara zabensa a 2019.

Sai dai Hafiz Ibrahim mashawarcin mataimakin shugaban kasar Yemi Osinbajo na musamman kan kafofin yada labarai ya ce an faro shirin na Tradermoni tun kafin karatowar zabe, haka zalika babu wata manufa a kasa ta tilastawa wadanda suka amfana da shirin zaben shugaba Muhammadu Buhari.

A cewar Hafiz Ibrahim shirin bai damu da sanin ko dan wanne jam'iyya ne ya ci gajiyarsa ba, haka zalika bai damu da bibiyar wacce jam'iyya za su zaba yayin zaben na 2019 ba.

Hafiz Ibrahim ya alakanta zarge-zargen na Bukola Saraki da Yakubu Dogara a matsayin farfagandar siyasa don yawo da hankalin al'ummar kasa. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.