Najeriya-Zabe

INEC za ta sake amfani da Card Reader a zaben Najeriya na 2019

Farfesa Mahmud Yakubu shugaban hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC.
Farfesa Mahmud Yakubu shugaban hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC. Ventures Africa

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta tabbatar da shirin sake amfani da na'urar tantance masu kada kuri'a da ake kira ‘Card Reader’ domin amfani da ita a zaben kasar na shekara mai zuwa.

Talla

Shugaban hukumar zaben Farfesa Mahmud Yakubu ya bayyana matakin da cewa zai taimaka matuka wajen gudanar da sahihancin zabe a Najeriyar.

Da ya ke tabbatar da matakin Mataimakin Daraktan yada labaran Hukumar ta INEC Aliyu Bello a zantawarsa da sashen hausa na Rediyo France International rfi ya ce hukumar ta amince da matakin ne don tabbatar da ba a samu magudi a zaben na 2019 ba.

Najeriya wadda a baya ta yi kaurin suna wajen magudin zabe a zaben shekarar 2015 ne ta fara amfani da na'urar ta Card Reader karkashin shugaban hukumar INEC Attahiru Jega, zaben da aka bayyana da mafi sahihanci a tarihin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI