Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo

Yara da dama sun kamu da cutar Ebola a Congo

Wasu ma'aikatan kiwon lafiya a Congo
Wasu ma'aikatan kiwon lafiya a Congo Photo: John Wessels/AFP

Majalisar dinkin Duniya tace kashi daya bisa uku na mutanen da suka kamu da cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo yara kanana ne, yayin da wasu da dama kuma suka zama marayu.Hukumar UNICEF tace alkaluman da suka tattara tare da abokan aikin su sun nuna cewar sama da yara 400 suka zama marayu tun bayan barkewar cutar.

Talla

Daraktar hukumar dake kula da Afrika ta Tsakiya da Afirka ta yamma, Marie-Pierre Poirier tace sun kadu sosai dangane da labarin cewar yara da dama sun kamu da cutar.

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta bayyana annobar cutar Ebola da ta sake barkewa a Jamhuriyar Congo a matsayin wadda ke mataki na biyu mafi muni a tarihi, bayan annobar cutar da ta hallaka dubban jama’a a Afrika ta Yamma cikin shekarun baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI