Wasanni

Morocco ta musanta neman karbar bakuncin gasar AFCON

Ministan wasannin kasar Morocco Rachid Talbi Alami.
Ministan wasannin kasar Morocco Rachid Talbi Alami. Getty Images

Ministan wasannin Morocco, Rachid Talbi Alami, ya ce kasarsa ba ta cikin kasashen dake neman hukumar CAF ta basu damar karbar bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa ta nahiyar Afrika AFCON ta 2019.

Talla

Ministan ya bayyana haka ne yayin zantawa da kamfanin dillancin labaran Faransa AFP.

A watan da ya gabata ne hukumar kula da kwallon Afrika CAF, ta kwace damar karbar bakuncin gasar ta AFCON daga hannun Kamaru, bisa dallilai na rashin kammala manyan ayyuka da kuma matsalolin tsaro.

Kafin kalaman ministan wasannin na Morooco rahotanni sun sha bayyana kasarsa da kuma Afrika ta Kudu, a matsayin kasashen dake kan gaba wajen zawarci ba su damar karbar bakuncin gasar cin kofin nahiyar ta Afrika.

Gasar ta AFCON mai zuwa a watannin Yuni da Yuli a 2019, ita ce ta farko da kasashe 24 za su fafata a cikinta, maimakon kasashe 16 da suka saba halartar gasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI