Najeriya-UNICEF

Rundunar Sojin Najeriya ta janye korar UNICEF daga arewa maso gabas

Rundunar sojin Najeriya ta janye haramcin da ta dora kan ayyukan Asusun UNICEF, wanda a baya ta zarga da yiwa yaki da ta'addanci zagon kasa.
Rundunar sojin Najeriya ta janye haramcin da ta dora kan ayyukan Asusun UNICEF, wanda a baya ta zarga da yiwa yaki da ta'addanci zagon kasa. AFP/File

Rundunar sojin Najeriya ta janye korar da ta yiwa Asusun tallafawa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF daga arewa maso gabashin kasar bisa zarginsa da yiwa yaki da ta’addanci zagon kasa.

Talla

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito mataimakin Daraktan yada labaran rundunar, Kanal Onyema Nwachukwu na cewa, matakin janye haramcin ayuukan a daren jiya Juma’a, ya biyo bayan tattaunawar da suka yi da wakilan asusun na UNICEF bisa shiga tsakanin wasu adalai.

A dai ranar ta Juma’a ce rundunar sojin Najeriya ta zargi UNICEF da cewa a maimakon taimakawa yara da sauran mabukata a rikicin Boko Haram ya shafa, asusun yana fakewa wajen shirya tarukan da ke zagon kasa ga yakar ta’addancin da sojin ke yi, dan haka an dakatar da aikin asusun har sai abinda hali yayi.

Kanal Onyema ya gargadi sauran kungiyoyin da ke aikin a Yankin da su yi taka tsan tsan wajen tsayawa kan aikin da aka amince musu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI