Faransa-Mali

Betancourt ta bukaci Shugaba Macron ya taimaka wajen sako Petronin

Sophie Pétronin yar kasar Faransa da ake garkuwa da ita a yankin Sahel
Sophie Pétronin yar kasar Faransa da ake garkuwa da ita a yankin Sahel © AFP

Ingrid Betancourt wadda ta shafe kusan shekaru shida a hannu yan tawayen Colombia na FARC daga shekara ta 2002 zuwa 2008 ta bukaci Shugaban Faransa Emmanuel Macron da ya sa bakin sa don gani an sako Sophie Petronin dake hannun yan tawayen arewacin Mali.

Talla

Betancourt ta jaddada cewa a zamanin tsohon Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy, tsohon Shugaban kasar ya taimaka sosai don gani an sako ta.

Yan tawayen Arewacin Mali sunyi awon gaba da Sophie Petronin mai shekaru 73 a Duniya ranar 24 ga watan Disamba na shekara ta 2016 a garin Gao dake arewacin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.