Gwamnatin Nijar ta kaddamar da shirin kawo karshen wutar daji

Sauti 19:52
Wutar daji
Wutar daji AAP/Dan Himbrechts/via REUTERS

A yau shirin namu zai duba batun wutar daji dake zama babbar matsala ga makiya sakamakon lakume abincin dabbobi da take, sannan da bata yanayi ta hanyar hallaka tsirai haka da wasu kananan namun daji.

Talla

A shekarar data gabata dai makiyaya a arewacin Nijer sun sha wahala sosai sakamakon rashin ciyawa, wannan kuma bayan wutar daji sama da 100 da aka samu da ta lakume dubunan Kadada na ciyawar dabbobi, babbar dabba na bukatar kadada uku ta ciyawa a shekara don rayuwa, lura da dubunan dabbobi da Allah ya horewa Nijer ciyar dasu ta hanyar sayen abinci abune da kamar wuya, damina mai kyau da aka samu a bana ta bayar da damar samun ciyawa mai yawa a dajin kiwo dake arewacin jihar Maradi cewa da yankunan gadabeji da bermo, wurin da dabbobi daga Agades, Tawa, da Zinder ke zuwa kiwo baya ga na jihar Maradi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI