Jamhuriyar Congo

Jaririya ta kafa tarihin warkewa daga cutar Ebola

Hoton jaririya Benedicte da asusun UNICEF, wadda ta warke da cutar Ebola, bayan haihuwarta tare da cutar a garin Beni. 3/12/2018.
Hoton jaririya Benedicte da asusun UNICEF, wadda ta warke da cutar Ebola, bayan haihuwarta tare da cutar a garin Beni. 3/12/2018. Guy Hubbard/UNICEF via AP

Wata jaririya mai wata guda da rabi a duniya, ta kafa tarihin zama mafi kankantar wadda ta harbu da Ebola ta kuma warke daga cutar a Jamhuriyar Congo.

Talla

Kakakin ma’aikatar lafiyar kasar Jessica Ilunga, ta ce jaririyar mai suna Benedicte ta kamu da cutar ta Ebola ce daga mahaifiyarta, wadda ta rasu yayin haihuwarta ta, itama a dalilin kamuwa da cutar ta Ebola.

Tun daga lokacin ne aka dora jaririyar kan kulawar likitoci babu kakkautawa, kuma a cewar ma’aikatar lafiyar yanzu haka tana tare da mahaifinta da sauran iyalai.

Zuwa yanzu dai, sama da mutane 300 suka rasa rayukansu a dalilin cutar Ebola da ta sake bulla a Jamhuriyar Congo cikin watan Agustan wannan shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.