Masar da Afrika ta Kudu na takarar karbar bakuncin gasar AFCON
Wallafawa ranar:
Hukumar kula kwallon kafa ta Afrika CAF, ta ce gasar cin kofin nahiyar dake tafe a 2019 wato AFCON, za ta gudana ne a kasar Masar ko kuma Afrika ta Kudu.
CAF wadda ta bayyana haka a karshen mako, ta ce kasashen guda biyu ne kawai suka mika bukatar neman karbar bakuncin gasar ta AFCON, kafin rufe karbar neman damar daga kasashe a daren ranar Juma’a.
Dukkanin kasashen na Masar ta Afrika ta Kudu sun taba karbar bakuncin gasar kwallon ta nahiyar Afrika sau biyu a baya.
Afrika ta Kudu ta karbi bakuncin gasar ce a shekarun 1996 da kuma 2013 a lokacin da ta maye gurbin Libya.
Masar kuwa ta taba karbar bakuncin gasar ce a shekarar 1986 da 2006.
Rahotanni a baya sun nuna cewa kasashen Ghana, Congo-Brazzaville, da Morocco sun nuna muradin karbar bakuncin gasar sai dai basu bayyana hakan a hukumance ba.
A watan da ya gabata, hukumar ta CAF ta karbe damar da ta baiwa kasar Kamaru na karbar bakuncin gasar, bisa dalilan gaza kammala shirin gine-gine da kuma matsaloli na tsaro.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu