Faransa-Burkina Faso

Faransa ta kai dauki zuwa Burkina Faso

Le président burkinabè Roch March Christian Kaboré et le président français Emmanuel Macron à l'entrée de l'Elysée, le 17 décembre 2018.
Le président burkinabè Roch March Christian Kaboré et le président français Emmanuel Macron à l'entrée de l'Elysée, le 17 décembre 2018. ludovic MARIN / AFP

Shugaban Burkina Faso Christian Kabore ya kai ziyara a Faransa inda ya tattauna da shugaban kasar ta Faransa Emmanuel Macron dangane da matsalar tsaron da kasar mai iyaka da Mali ke fama da ita.

Talla

Faransa tsawon shekaru na taka gaggarumar rawa wajen dafawa kasashen Sahel a bangaren tsaro, tareda samar da kungiyar nan ta G5 Sahel da Nijar ke jagoranta, sai dai hakan bai hana yan ta’adda cigaba da kai hare-hare zuwa kasashen da suka hada da Burkina Faso.

karshen ganawar Shugaban Burkina Faso da Emmanuel Macron na Faransa , Faransa ta ce za ta bai wa jami’an tsaron Burkina Faso motocin Pick-up 34 domin karfafa masu gwuiwar yaki da ayyukan ta’addanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.