Najeriya

Karin mutane 37 za su fuskanci haramcin balaguro a Najeriya

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari. Audu MARTE / AFP

Gwamnatin Najeriya ta mikawa hukumar shige da fice ta kasar jerin sunayen mutane 39 da ta ke zargi da wawure dukiyar al’umma inda ta nemi hukumar da ta dauki matakan haramta masu ficewa daga kasar.

Talla

A cewar Cheif Okoi Obono-Obla shugaban kwamitin da gwamnatin ta kafa don tattara sunayen mutanen da ake zargi da almundahanar kudade a Najeriyar, ya ce za a dauka matakan da suka dace kan mutanen 37.

Ko da dai kawo yanzu jerin ilahirin sunayen mutanen bai kammala fitowa ba, amma kwamitin ya ce ya kunshi wadanda ake bincike a kansu ciki har da dan takarar neman kujerar Gwamna a jihar Imo karkashin Jam’iyyar APC, tsohon shugaban Majalisar Dattijai David Mark da tsohon shugaban Majalisar Wakilai Dimeji Bankole.

Obono-Obla ya tabbatar da umarnin gwamnatin ga hukumar ta NIS kan ta haramtawa mutanen damar fita daga Najeriya sakamakon wawuson da suka yiwa dukiyar kasa.

He further revealed that the panel, in partnership with the Nigerian Intelligence Agency, isinvestigating Nigerians allegedly implicated in the Paradise Panama Papers. Hesaid the “findings would be made available to Nigerians; in due course.

A cewarsa, kwamitin da taimakon hukumar leken asiri ta Najeriya na gudanar da binciken kwakwaf game da tarin dukiyar da ke Panama wanda ya ce nan gaba kadan za su fitar da cikakken bayani kan batun.

Kwamitin ya kuma bayyana cewa, yanzu haka cikin jerin wadanda ya ke bincika akwai Iyalan Tumsah da suka hadar da Tijani Tumsah , mataimakin shugaban shirin farfadowa da yancin arewa maso gabas na gwamnatin Tarayya da Ibrahim Tumsah daraktan kudi na ma’aikatar lantarki ayyuka da gidaje wadanda dukkaninsu ake zargin kan cin hanci da rashawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI