Najeriya

Kungiyar Amnesty na kawo cikas ga batun tsaro a Najeriya

Tambarin kungiyarAmnesty International
Tambarin kungiyarAmnesty International Amnesty

Rundunar sojin Najeriya ta bukaci rufe ofishin kungiyar Amnesty International saboda abinda ta kira yunkurin wargaza kasar.Sanarwar da daraktan yada labaran rundunar Janar Sani Usman Kukasheka ya bayar, tace kungiyar na daukar nauyin wasu kungiyoyin mutanen da ke yiwa kasa zagon kasa da kuma neman batawa sojojin suna.

Talla

Rundunar Sojin Najeriya a baya ta sanar da dakatar da ayukan hukumar kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya saboda abinda ta kira wasu ayyukan dake yiwa yaki da ta’addanci zagon kasa,kafin daga bisali ta soke matakin,bisa zargin hukumar UNICEF da barin aikin da ya rataya akan ta tareda taimakawa yara da mabukata wajen shirya tarurrukan dake zagon kasa ga aikin sojin.

Matakin dakatar da ayukan Amnesty na zuwa ne kwanaki biyu bayan janye dakatarwar da aka yiwa kungiyar UNICEF.

Dangane da wannan mun tuntubi Isa Sanusi, mai Magana da sunan Amnesty a Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI