Muhammad Hashim Suleiman na Jami'ar Ahmadu Bello kan hukuncin shekaru 2 a yari ga malamin jami'ar Obafemi da ya nemi lalata da Daliba

Sauti 03:53
Tuni wasu suka fara korafi game da hukuncin kotun inda su ke ganin kamata ya yi hukuncin ya zarta shekaru 2.
Tuni wasu suka fara korafi game da hukuncin kotun inda su ke ganin kamata ya yi hukuncin ya zarta shekaru 2. Naij.com

Wata Kotu a Najeriya ta daure wani malamin Jami’ar Obafemi Awolowo shekaru biyu a gidan yari, saboda samun sa da laifin bukatar lalata da wata dalibar sa kafin ba ta makin jarabawa.Mai shari’a Maurine Onyetenu tace malamin Farfesa Richard Akindele ya ci amanar da aka bashi, inda ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 2 a gidan yari. Dangane da wannan hukunci, mun tattauna da Malam Muhammad Hashim Suleiman, da ke koyarwa a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, kuma ga tsokacin da yayi akai.