"Kamfanonin jiragen saman Afrika za su yi hasarar dala miliyan 300"

Shugaban hukumar kula da sufurin jiragen sama ta duniya (IATA) Alexandre de Juniac.
Shugaban hukumar kula da sufurin jiragen sama ta duniya (IATA) Alexandre de Juniac. REUTERS/Pierre Albouy

Hukumar lura da sufurin jiragen sama ta duniya IATA, ta bayyana hasashen cewa, kamfanonin jiragen sama da ke kasashen nahiyar Afrika ciki har da Najeriya, za su tafka hasarar dala miliyan 300 a cikin shekarar 2019 mai kamawa.

Talla

Hukumar ta IATA, ta ce kamfanonin jiragen saman za su tafka hasarar ce, duk da cewa akwai hasashe mai karfi da ke nuna cewa sashin sufurin jiragen saman duniya zai samu ribar akalla dala biliyan 35 da miliyan 500 a dai shekarar ta 2019.

Ko da yake, hukumar kula da sufurin jiragen saman ta duniya, ba ta fayyace dalilan da za su haddasawa kamfanonin Afrika hasarar ta dala miliyan 300 ba, masana na kallon al’amarin da cewa ba zai rasa nasaba da batu na tattalin arziki da zuba hannayen jari ba.

Sai dai duk da haka, IATA ta yi hasashen cewa shekarar ta 2019 za ta fi armashi ga kamfanonin sufurin jiragen saman Najeriya da sauran takwarorinsu na Afrika, la’akari da cewa a shekarar 2018 mai karewa kadai sun tafka hasarar dala miliyan 400.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI