Nijar

An rufe makarantu a Nijar sabili da rashin tsaro

Jami'an tsaro a wasu yankunan  da ake fuskantar matsalar tsaro a Tillabery
Jami'an tsaro a wasu yankunan da ake fuskantar matsalar tsaro a Tillabery RFI

A Jamhuriyar Nijar, adadin makarantun bokon da aka rufe sakamakon matsalar tsaro a halin yanzu sun kai dari daya.Ofishin kula da ayyukan jinkai na Majalisar Dinkin Duniya a birnin Yamai ya ce a jihar Tillaberi da ke yammacin kasar kawai an dakatar da ayyukan makarantu 33 yayin da wasu 18 suke rufe baki daya saboda rashin tsaro a yankin mai iyaka da Mali da Burkina Faso.

Talla

A yan watanni da suka gabata Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da wasu alkaluma dangane da yawan yan gudun hijira da suka tsere daga wasu yankunan arewacin Mali kama daga farkon watan Janairu zuwa wannan lokaci.

A wannan rahoto hukumar ta bayyana irin kokarin da jami’an ta ke yi dama irin kalubalen dake gaban ta.

Kama daga farkon shekarar nan sama da yan gudun hijira 17.000 ne suka samu rijista daga hukumar dake kula da yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya a yammacin Nijar.

Yan gudun hijira da aka sarin su tabarbarewar tsaro a wani yankin na kasar Mali ya tilastawa baro matsugunin su.

Jami’an dake bada kulawa zuwa yan gudun hijirar sun bayyana cewa kusan mutane 17.382 ne suka gudo domin cira da rayukan su daga hare-haren mayakan jihadi, banda haka mutanen da rikicin kabilanci ya tilasatawa canza wurin zama zuwa garuruwa a yankin Tillabery a cewar ofishin hukumar dake kula da ayukan jinkai na OCHA.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI