ECOWAS

'ECOWAS na bukatar gaggauta samar da kudin bai-daya'

Shugaba Buhari na Najeriya ya jagoranci taron shugabannin kasashen Afrika ta Yamma a Abuja
Shugaba Buhari na Najeriya ya jagoranci taron shugabannin kasashen Afrika ta Yamma a Abuja FEMI ADESINA

Kwamatin da Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Yammacin Afrika, ECOWAS ta kafa domin lalubo mata dalilin da ya sa kasuwanci tsakanin kasashen kungiyar ke samun koma-baya, ya bayyana rashin samar da kudin-bai-daya a matsayin babbar matsalar da ke hana cinikayya samun nasara a yankin.

Talla

Kwamitin ya bayyana haka ne a wani rahoto da ya mika wa shugabannin kungiyar a yayin gudanar da taronsu karo na 54 a birnin Abuja karkashin jagorancin shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari.

A yayin zantawa da manema labarai, Ministan Harkokin Wajen Nijar kuma daya daga cikin mambobin kwamitin Kalla Hankurau, ya ce, lallai akwai bukatar gaggauta samar da kudin na bai daya don bunkasa tattalin arzikin yankin.

Kalla Hankurau kan taron Ecowas a Abuja

Hankurau ya alakatan nasarar harkokin kasuwanci a kasashen Turai da amfani da kudin bai-daya.

A yayin gabatar da jawabin bude taron, shugaba Buhari mai masaukin baki, ya bukaci shugabannin kungiyar da su biya hukumominsu kudaden da doka ta ce a ba su don ci gaba da aiwatar da shirin hadin-kan kasashen yankin na yammacin Afrika.

Baya ga batun matsalar tattalin arziki, shugabannin sun tattaunawa kan al’amuran da suka shafi rikice-rikicen siyasa a yankin

A bangare guda, shugaba Buhari ya jaddada aniyarsa ta gudanar da sahihin zaben shugaban kasa a shekara mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI