Najeriya

Rundunar 'Yan sandan Najeriya ta yaye kurata dubu 6

Babban Sufeton 'Yan sandan Najeriya Ibrahim Idris.
Babban Sufeton 'Yan sandan Najeriya Ibrahim Idris. Daily Post Nigeria

Babban sufeton ‘yan sandan Najeriya Ibrahim Idris ya ce akalla kuratan ‘yan sanda dubu 6 aka yaye bayan sun samu horon watanni 7 a kwalejojin horar da ‘yan sanda na Maiduguri da Enugu da kuma Minna wadanda yanzu haka za a rarrabasu a sassan kasar don aikin tabbatar da tsaron al’umma.

Talla

A cewar Ibrahim Idris yayin taron yaye kuratan da ya tura wakilci a kwalejojin 3, adadin wani bangare ne na ‘yan sanda dubu 10 da gwamnati mai ci ta sha alwashin samarwa da nufin karfafa tsaro a sassan Najeriyar.

Babban Sufetonn’yan sandan Najeriyar, ya ce ‘yan sandan wadanda dukkaninsu matasa ne masu jini a jika sun samu cikakken horon da za su bayar da gudunmawar da ta kamata, musamman a halin da kasar ke ciki na tabarbarewar al’amuran tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI