Jamhuriyar Congo

Za a yi zabe a yankunan da Ebola ta bulla - CENI

Wasu jami'an kula da lafiya da ke lura da masu dauke da cutar Ebola a  Jamhuriyar Congo.
Wasu jami'an kula da lafiya da ke lura da masu dauke da cutar Ebola a Jamhuriyar Congo. John Wessels/AFP

Hukumar zaben Jamhuriyar Congo CENI, ta bada tabbacin zabe zai gudana ranar 30 ga watan Disamba da muke ciki, a yankin arewa maso gabashin kasar da cutar Ebola ta sake bulla.

Talla

Kakakin hukumar zaben Jean-Pierre Kalamba ne ya bayyana haka, duk da cewa wasu na fargabar bude rumfunan zabe a wuraren da Ebolar ta sake bayyana ka iya haddasa kamuwar karin wasu mutane da cutar.

Sai dai ma’aikatar lafiyar kasar ta ce za’a dauki matakan baiwa mutane kariya, da ya hada da sanya masu zabe wanke hannu kafin kada kuri’a.

Wani rahoton hukumar lafiya ta Duniya WHO ya ce daga 28 ga Nuwamba zuwa yanzu, sama da mutane 500 aka tabbatar sun kamu da cutar ta Ebola a arewacin lardunan Kivu da Ituri, zalika bayan sake bullar cutar a watan Mayu zuwa yanzu mutane 320 suka hallaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI