'Yan awaren kamaru sun kaddamar da samfurin kudin Intanet
Wallafawa ranar:
‘Yan awaren kasar Kamaru sun kaddamar da wani samfurin kudi da ake hada-hadarsa ta shafin Intanet da su ka yi wa suna Ambacoin, a wani mataki na karfafa gwargwarmayarsu ta kafa kasar Ambazonia.
Darajar kudin wanda yanzu haka ya ke kasa da daya bisa hudun dalar Amurka, shugabannin gwagwarmayar ‘yan awaren na ganin zai taimaka musu matuka wajen fadada farfagandar su baya ga samar da kudaden shiga a fafutukar da su ke.
Bayan kaddamar da samfurin kudin a yau Litinin, akalla mutane dubu 28 suka mika bukatar sayensa matakin da ke nuna karbuwar kudin ga jama’a.
Tun a ranar 1 ga watan Oktoban shekarar 2017 ne 'yan awaren suka tabbatar da samun yanci kai daga Kamaru tare da radawa sabuwar kasar ta su Ambazonia, matakin da yanzu haka ke ci gaba haddasa tashe-tashen hankula a kasar ta Kamaru.
Tuni dai yankin ya samarwa kansa Tuta baya ga nada shugaba ko da dai tuni gwamnati Kamaru ta yi watsi da shi tare da aikewa da tarin sojojin don tunkrar mayakan na 'Yan aware.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu