'Mutane 37 sun mutu saboda farashin burodi a Sudan'
Wallafawa ranar:
Kungiyar Kare Hakkin Bil’adama ta Amnesty International ta ce, ta samu wasu bayanai da ke cewa, jami’an tsaron Sudan sun harbe mutane 37 har lahira a yayin kokarin tarwatsa masu zanga-zangar adawa da tsadar farashin burodi a sassan kasar.
Tun a ranar Larabar da ta gabata aka fara gudanar da zanga-zangar bayan gwamnatin kasar ta ninka farashin buredin har sau uku.
Mahukuntan kasar sun ce, akalla masu zanga-zanga 8 aka kashe, yayin da shugaban babbar jam’iyyar adawa, Sadiq al-Mahdi ya ce, adadin ya kai 22.
Sai dai a cewar Amnesty, rahotannin da ta samu daga majiyoyi kwarara sun ce, mutane 37 jami’an tsaron kasar suka kashe a cikin kwanaki biyar na zanga-zangar.
Darektar Amnesty a gabashin Afrika, Sarah Jackson ta ce, abin damuwa ne yadda jami’an tsaron ke amfani da karfin da ya wuce kima kan masu zanga-zangar da ba sa dauke da makamai.
Jackson ta bukaci gwamnatin kasar da ta kawo karshe amfani da karfin da ya wuce kima don kauce wa ci gaba da zubar da jini.
Har yanzu, gwamnatin Sudan ta ba mayar da martini ba game da rahoton na Amnesty International, yayin da shugaban kasar Omar Al-Bashir ya lashi takobin samar da sauye-sauye da zummar kwantar da hankula a kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu