Isa ga babban shafi
Najeriya-Boko Haram

'Yan sandan Najeriya 190 sun tsere saboda tsoron yaki da Boko Haram

Rahotannin sun ce 'yansandan 190 sun samu labarin cewa ana gab da tura su yankunan da ake yaki da Boko Haram, dalilin da ya tilasta musu tserewa.
Rahotannin sun ce 'yansandan 190 sun samu labarin cewa ana gab da tura su yankunan da ake yaki da Boko Haram, dalilin da ya tilasta musu tserewa. punch.com

Rahotanni daga Najeriya na cewa, jami’an ‘yan sandan kasar 190 sun tsere daga horon da ake ba su na musamman a wata makarantar horas da sojoji da ke garin Buni Yadi na jihar Yobe a yankin arewa maso gabashin kasar.

Talla

Tserewar Jami'an na zuwa ne bayan wasu bayanai da ke nuna cewa, ana shirin tura su wuraren da ake kan ganiyar fama da rikicin Boko Haram da suka hada da kan iyakokin Chadi da Nijar.

Adadin dai wani bangare ne na 'yansanda dubu 2 da babban Sufeto Janar na ‘yan sandar kasar, Ibrahim Idris ya yi alkawarin bayarwa don taimakawa sojoji wajen yaki da mayakan Boko Haram.

Tuni dai shalkwatar 'Yan sandan ta yi umarnin kame mutanen 190 don fuskantar hukunci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.