Najeriya-Zamfara

Rikicin Zamfara ka iya haifar da karancin abinci a Najeriya

A bayanan da ta fitar, gwamnatin Najeriyar ta kuma musanta kisan wasu masu zanga-zanga da ake zargin sojinta da aikatawa a jihar ta Zamfara.
A bayanan da ta fitar, gwamnatin Najeriyar ta kuma musanta kisan wasu masu zanga-zanga da ake zargin sojinta da aikatawa a jihar ta Zamfara. post-nigeria.com

Gwamnatin Najeriya ta hannun Ministan cikin Gidanta Laftanar Janar Abdurrahman Dambazau mai ritaya, ta ce akwai yiwuwar hare-haren da ‘yan bindiga suka matsa  kai wa Zamfara ya iya haddasa matsalar karancin abinci da za ta shafi fadin Najeriyar.

Talla

Gwamnatin Najeriyar ta hannun ministan tsaronta Mansur Dan-Ali ta kuma musanta cewa sojojin kasar sun bude wuta kan wasu masu zanga-zanga nuna bikin cikin hare-haren ‘yan bindigar a jihar ta Zamfara inda suka hallaka wasunsu a ranar Kirsimeti.

Ministocin sun bayyana haka ne yayin ziyarar da suka kai jihar ta Zamfara domin ganewa idanunsu halin da sha’anin tsaro ke ciki da kuma daukar matakan kawo karshen lamarin.

Rikicin Zamfara ka iya haifar da karancin abinci a Najeriya

Wakilinmu Faruk Muhd Yabo yana dauke da karin bayani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI