Madagascar

Andry Rajolina ya lashe zaben kasar Madagascar

Andry Rajolina
Andry Rajolina RIJASOLO / AFP

Tsohon shugaban kasar Madagascar Andry Rajoelina ya lashe zaben shugaban kasar a zagaye na biyu a gaban Marc Ravalomanana.Rajoelina ya lashe zaben da fiye da kuri’u 55 a gaban abokin takara kuma tsohon Shugaban kasar Marc Ravalomanana, wanda ya samu kashi 44 na kuri’u da yan kai cikin dari.

Talla

Zaben na ranar 19 ga watan Disemba na shekara ta 2018 a cewar bangaren Marc Ravalomanana na tattare da magudi, a cewar tsohon shugaban kasar Marc Ravalomanana mai kuri’u 44,34 cikin dari ya bukaci kotu ta sake duba batun zaben a wasu mazabu.

A yayin da shi kuma Rajolina, wanda ya lashe zaben da kuri’u 55, 66 cikin dari, ya sanar da manema labarai cewa, al’ummar kasar Madagascar ta gudanar da zabi ne a cikin walwala da yanci, haka kuma ya yi fatan ganin ya tabbatar da kawo cikakken sauyin demokaradiyya a kasar.

Rajolina ya kara da cewa, an yanzu duk hankalin kasashen duniya na a kansu, don haka samar da cikakken sauyi a Madagaskar shi ne abin da zasu sa a gaba.

Rajolina mai shekaru 44, ya saurari sakamakon zaben ne daga hukumar da ke tsara zaben kasar CENI .

Shugaban hukumar Zaben, Rakotomanana ya bayyana rashin jin dadin sa, a game da cewa, lokacin da hukumarsa take bada sakamakon Marc Ravalomanana baya tare da su.

Gwamnatin kasar ta tura da yawan yan Sanda zuwa harabar hukumar zaben kasar don bayar da tsaro da ya dace dama dakile duk wani tshin hankali da kan iya kuno kai a lokacin fitar da sakamakon zaben kasar.

Yanzu dai hankalin jama’a ya karkata zuwa babbar kotun da ke kula da dokokin kasar, wacce ke da nauyin tabbatar da sahihancin zaben nan da kwanaki 9.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.