Masar

Yan Sanda sun kashe yan ta'adda 40 a Masar

Yan Sandan kasar Masar
Yan Sandan kasar Masar REUTERS/Amr Abdallah Dalsh

A wani samame da yan Sanda suka kai zuwa maboyar yan ta’ada a Masar kwana daya bayan wani kazamin hari da aka kai zuwa baki yan yawon bude ido yan kasar Vietnam, jami’an tsaron kasar sunyi nasarar kashe mayakan jihadi 40 a yau asabar.

Talla

A jiya juma’a ne wasu yan yawon bude ido uku yan kasar Vietnam suka rasa rayukan a wani harin bam da aka kai musu a dai dai lokacin da motar dake dauke da su ta isa wani wuri tarihin dake kudu maso yammacin kasar ta Masar.

Da sanar da mutuwar yan kasar ta, Vietnam ta bukaci hukumomin sun dau matakan da suka dace domin hukunta masu hannu a wannan kazamin aiki a cewar Ministan harakokin wajen Vietnam Lee Thi THU hANG,

Nan take Masar ta samu goyan bayan manyan kasashen Duniya da suka nuna alhinin bayan harin yan ta’adan.Kama daga watan Fabrairun shekarar bana dai ne gwamnatin kasar Masar ta sanar da kaddamar da farautar mayakan jihadi tareda samun nasarar kasha mayakan akalla 500.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.