Najeriya-Nijar

Harin 'yan bindiga ya hallaka sojin Nijar da na Najeriya a kan iyaka

A baya-bayan nan 'Yan bindiga a kan iyakokin kasashen biyu na barazana ga tsaro bayan hare-haren mayakan boko Haram a gefe guda.
A baya-bayan nan 'Yan bindiga a kan iyakokin kasashen biyu na barazana ga tsaro bayan hare-haren mayakan boko Haram a gefe guda. CNBC Africa

Rahotanni daga kan iyakar Najeriya da Nijar na cewa wata fafatawa tsakanin sojin kasashen biyu da 'yan bindiga ta kai ga rasa rayukan akalla sojoji 5 tare da jikkatar wasu da dama.

Talla

Ministan tsaron Nijar Kalla Moutari da ya ke tabbatar da fafatawar ya ce 'yan bindigar sun farmaki dakarun da ke aikin hadin gwiwa don bayar da tsaro akan iyakar Najeriya da Nijar matakin da ya kai su ga musayar wuta wanda ya yi sanadin mutuwar sojojin Najeriya 5 na Nijar 5.

A cewar Kalla Moutari yayin musayar wutar suma sojojin sun yi nasarar hallaka 'yan bindiga 11 akan iyakar kasashen biyu da ke gab da garin Maradi.

A baya-bayan nan 'Yan bindiga a kan iyakokin kasashen biyu na barazana ga tsaro bayan hare-haren mayakan boko Haram a gefe guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI