Najeriya-UNICEF

Za a haifi Jarirai fiye da dubu 25 gobe a Najeriya - UNICEF

Najeriya na cikin jerin kasashe 8 da za su wakilci rabin jariran da za a haifa a duniya baki daya ranar sabuwar shekara.
Najeriya na cikin jerin kasashe 8 da za su wakilci rabin jariran da za a haifa a duniya baki daya ranar sabuwar shekara. AFP/Oli SCARFF

Wani binciken asusun tallafawa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya nuna cewa za a haifi jarirai kimanin dubu 25 da 685 a gobe Talata 1 ga watan Janairun shekarar 2019.

Talla

A cewar Daraktan asusun na UNICEF shiyyar Najeriya Pernille Ironside a Najeriyar kadai za a haifi kashi 40 cikin dari na yaran da za a haifa a nahiyar Afrika gobe Talata.

Da ya ke jawabi ga kamfanin dillacin labaran kasar NAN a Abuja babban birnin Najeriyar, Mr Pernille ya ce kasar har wa yau na wakiltar kashi 6 da rabi na adadin yaran da za a haifa a duniya baki daya ranar sabuwar shekarar.

Cikin bayanan asusun na Unicef ya kuma bayyana cewa daga daren yau Litinin daga karfe sha biyu na dare zuwa gobe Talata har zuwa wata karfe sha biyun na dare za a haifi yara dubu dari 3 da 95 da 72 a duniya baki daya.

Rahoton ya nuna cewa haife-haife a kasashe 8 na duniya ne ciki har da Najeriya zai wakilci rabin haife-haifen da za a samu gobe a duniya baki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI