Shugaban Najeriya a Jamhuriya ta biyu, Alhaji Shehu Usman Shagari ya rasu

Sauti 20:06
Tutar Najeriya
Tutar Najeriya

A cikin shirin karshen shekara na 2018,Garba Aliyu Zaria ya mayar da hankali zuwa  labaren Najeriya,ta fuskar siyasa,tattalin arziki,kiwon lafiya da kuma zamantakewa.Garba Aliyu Zaria ya duba zancen rasuwar  Alhaji Shehu Shagari wanda shi ne Turakin Sokoto da ya yi mulkin Najeriya tsakanin shekara ta 1979 zuwa 1983.Ya mutu yana da shekaru 93 bayan rashin lafiya a babban Asibitin Abuja.