Burkina Faso

'Yan bindiga sun hallaka mutane 13 a Burkina Faso

Wani yanki a Burkina Faso.
Wani yanki a Burkina Faso. © Coralie Pierret / RFI

A Burkina Faso, wasu mahara sun hallaka mutane 13 a kauyen Yirgou da ke arewacin kasar, lamarin da ya haifar da zaman dar-dar a tsakanin mazauna yankin da ke fargabar barkewar rikicin kabilanci.

Talla

Hukumomin tsaron kasar ta Burkina Faso sun ce, maharan sun kai farmakin ne akan Babura, kuma cikin mutanen da suka hallaka, har da dagacin kauyen na Yirgou da kuma dansa.

A baya-bayan nan Burkina Faso na yawan fuskantar hare-haren 'yan bindiga da na mayaka masu ikirarin jihadi wanda a lokuta da dama ke haddasa asarar rayuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.