Libya

Libya ta bayar da sammaci kamo wasu yan tawaye

Hari da aka kai zuwa ofishin ministan harakokin wajen Libya
Hari da aka kai zuwa ofishin ministan harakokin wajen Libya REUTERS/Hani Amara

Hukumomin rikon kwariyar kasar Libya sun bayar da samacin kamo wasu mutane 37 da suka hada da yan kasar da wasu yan tawayen Chadi hade da Sudan bisa zargin su da kaddamar da hare-hare zuwa wasu masana’antun man kasar da barikokin sojan kasar Libya.

Talla

Sanarwar da hukumomin Libya suka fitar na zargin yan kasar ta Libya Shida da suka hada da wasu tsofin jagororin yan tawayen kasar Abdelhakim Belhaj da Ibrahim Jadhran da suka samu goyan bayan wasu yan tawaye daga Sudan da Chadi a wasu kazaman hare-hare zuwa wasu masana’antu mai dake gabacin kasar da wani barikin soja dake Tamenhant dake da nisan kilometa 500 da babban birnin kasar ,wanda ya kuma haddasa mutuwar mutane 140.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.