Sudan

'Yan sandan Sudan sun sake tarwatsa masu zanga-zanga

Wasu masu zanga-zanga a birnin Khartoum na Sudan.
Wasu masu zanga-zanga a birnin Khartoum na Sudan. Reuters

‘Yan sandan Sudan sun tarwatsa gungun masu zanga-zangar kin jinin gwamnati, da ke kan shirin sake yin tattaki zuwa fadar gwamnatin a Khartoum, don tilastawa shugaba al-Bashir yin murabus.

Talla

Yunkurin sake fita gagarumar zanga-zangar, ya zo ne bayan da a ranar Asabar, shugaba al-Bashir ya kori Ministan lafiyar kasar, saboda tsadar magunguna.

Tun a ranar 19, ga watan Disamban bara, zanga-zanga ta barke a wasu biranen Sudan ciki har da Khartoum, bayan karin farashin biredi da gwamnati ta yi, daga bisani kuma ta juye zuwa ta neman tilasatawa shugaba al-Bashir yin murabus.

Jami’an tsaron kasar sun ce kawo yanzu mutane 19 suka hallaka, ciki har da ‘yan sanda biyu, sai dai a nata rahoton, kungiyar Amnesty International ta ce yawan wadanda suka mutu, ya kai 37.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI