Gabon

An hallaka jagororin masu yunkurin juyin mulki a Gabon

Jagoran masu yunkurin juyin mulkin da mataimakansa biyu lokacin da suka kwace iko da gidan rediyon kasar.
Jagoran masu yunkurin juyin mulkin da mataimakansa biyu lokacin da suka kwace iko da gidan rediyon kasar. HANDOUT via Reuters

Hukumomin tsaro a kasar Gabon sun tabbatar da kisan biyu daga cikin sojojin da suka jagoranci yunkurin juyin mulkin kasar a yau Litinin baya ga kame jagoransu dai dai lokacin da kasashen duniya ke ci gaba da tir da matakin.

Talla

Bayanai na nuni da cewa wata tawagar jami’an soji ce ta isa gidan Rediyon da dakarun biyar suka kame inda suka hallaka biyu tare da kame jagoran, baya ga ceto ‘yan jaridun gidan rediyon wadanda sojojin masu yunkurin juyin mulkin suka tilasta musu yada manufarsu.

Yanzu haka dai dubban al'umma ne suka yi dandazo a sassan kasar don nuna goyon bayansu ga yunkurin juyin mulkin na soji sakamakon tsawon lokacin da shugaban kasar Ali Bongo ya dauka yana jinya a ketare.

Sai dai tuni kasar Faransa da kungiyar Tarayyar Afrika suka yi gargadi game da illar da juyin mulkin ka iya haifarwa kasar ta Gabon wanda suka kira da yunkurin garambawul ga tanadin kundin tsarin mulkin kasar.

Cikin wani sakon Twitter, shugaban kungiyar Tarayyar Afirka Musa Faki Mahamat ya ce kungiyar ta yi tir da yunkurin juyin mulkin a Gabon yayin da ta nemi kwantar da hankali a kasar.

A bangare guda ita ma Faransa wadda ta mulki Gabon daga 1885 har zuwa 1960, ta ce ba ta goyon bayan duk wani yunkurin sauya gwamnati ba ta hanyar da doka ta amince ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.