Isa ga babban shafi
Gabon

Al'amura sun daidaita a Gabon

Jami'an sojin Gabon a gaban gidan rediyo da na talabijin na gwamnatin kasar
Jami'an sojin Gabon a gaban gidan rediyo da na talabijin na gwamnatin kasar Steve JORDAN / AFP
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad
1 Minti

Mahukunta a kasar Gabon sun ce a halin yanzu lamurra sun daidaita, bayan da wasu sojoji da aka bayyana adadinsu a matsayin 10 suka yi yunkurin kifar da gwamnatin shugaba Ali Bongo Odingba da ke jinya a kasar Maroko.

Talla

Mahukunta a birnin Libreville sun ce, an kashe biyu daga cikin sojojin biyu, yayin da aka cafke sauran cikinsu har da jagoransu laftana Ondo Obiang Kelly, wanda ya karanta sanarwa juyin mulkin a gidan rediyo da talabijin na kasar.

Jakadan kasar a birnin Paris Flavien Enongu ya ce, tuni aka fara bincike domin tantance wadanda ke da hannu a yunkurin.

Enongu ya ce, "Gabon kasa ce da ke aiki da doka saboda an fara bincike, kuma tabbas za a gano wadanda ke da hannu a wannan lamari, daga cikin sojoji watakila ma har da ‘yan siyasa."

"Akwai wadanda tuni suka fara murna alhali kuwa kamata ya yi a nuna damuwa idan kasa ta shiga cikin wannan hali." In ji Enongu.

Jakadan ya kara da cewa, "Wadannan ‘yan siyasa ne da a kullum ke murna da farin ciki idan kasarsu ta shiga a cikin yanayi na damuwa."

An dai samu wasu mutane da suka bazama kan tituna suna murna da yunkurin juyin mulkin, yayin da kasashen duniya da suka hada da Kungiyar Tarayyar Turai suka gargadi girmar illa da juyin mulkin zai iya haifar wa a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.