Moussa Aksar kan nasarar Felix Tshisekedi a zaben Jamhuriyar Congo

Sauti 03:21
Fitaccen dan jarida kuma marubuci a Jamhuriyyar Nijar Mousa Aksar.
Fitaccen dan jarida kuma marubuci a Jamhuriyyar Nijar Mousa Aksar. Reuters

Hukumar zaben Jamhuriyar Congo ta bayyana dan takarar adawa Felix Tshisekedi, a matsayin wanda ya lashe zaben shugabancin kasar da aka yi ranar 30 ga watan disambar sa ya gabata.Wannan ne dai karon farko a tarihi, da dan takarar adawa ya yi nasarar kayar da dan takarar jam’iyya mai mulki a a kasar, to sai dai tuni Martin Fayulu, wanda ya tsaya zabebn karkashin inuwar wata jam’iyyar ta adawa, ya yi zargin cewa an tafka magudi. Abdoulkarim Ibrahim Shikal, ya zanta da shahrarren marubuci wanda kuma ya san salon siyasar kasar ta Congo wato Moussa Aksar, dangane da wannan sakamako, ga kuma zantawarsu.