Najeriya-Boko Haram

Rundunar Sojin Najeriya ta sake kwato garin Baga na jihar Borno

Fiye da mutane dubu 27 hare-haren Boko Haram ya hallaka a garin Baga yayinda wasu kuwan miliyan biyu suka rasa matsugunansu.
Fiye da mutane dubu 27 hare-haren Boko Haram ya hallaka a garin Baga yayinda wasu kuwan miliyan biyu suka rasa matsugunansu. AFP PHOTO / REINNIER KAZE

Rahotanni daga garin Baga na jihar Borno na cewa yanzu haka jami'an sojin kasar sun kwace iko da garin wanda a baya ya koma karkashin ikon mayakan Boko Haram.

Talla

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito wani sojin Najeriya na cewa dakarun sun kutsa kai cikin garin na baga a yammacin jiya Laraba inda suka fatattaki mayakan na Boko Haram.

Matakin sake kwace iko da garin na Baga na zuwa dai dai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ke cewa akwai fiye da mutane dubu 30 da yanzu haka su ka fice daga garin na Baga don kaucewa mulkin Boko Haram bayan da ta kwace iko da garin.

Wasu hare-haren mayakan na Boko Haram kan sansanonin sojin Najeriyar a Baga cikin makwannin da suka gabata wanda suka kai ga kisan da dama ne ya bai wa Boko Haram damar kwace iko da garin.

Wani ganau ya shaidawa manema labarai cewa da misalin karfe 5 da rabi na yammaci lokacin da ya ke kokarin yin hijira daga garin ya ga jerin gwanon motocin sojoji sun yi wa garin tsinke, inda kai suka yi sansani a Kuros-Kauwa mai tazarar kilomita 15 kafin afkawa Baga da misalin karfe 7 na dare.

Rahotanni na nuni da cewa tun bayan fara ayyukan ta'addancin Boko Haram a 2009 akalla mutane dubu 27 hare-haren Boko Haram ya hallaka a iya garin Baga yayinda wasu miliyan 2 suka rasa muhallansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.